26 Agusta 2024 - 16:09
Yahudawa Na Shirin Gina Majami'an A Cikin Masallacin Qudus

Ben Gweir yana neman gina majami'a a cikin Masallacin Al-Aqsa inda ya sha suka akan maganganunsa

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti As Abna ya habarto maku bisa nakaltowa daga shafin Qudus cewa: A cikin wani sabon yunkuri kuma mai hatsarin gaske, ministan tsaron cikin gidan gwamnatin sahyoniyawa Itmar Ben Guer ya ce nan ba da jimawa ba zai gina wata majami'ar Yahudawa a cikin masallacin Al-Aqsa.

Ya ce: Manufofinmu na siyasa sun halatta yin sallah a kan Dutsen Haikali (Masallacin Al-Aqsa). Domin Doka daidai take ga Yahudawa da Musulmai kuma ina da niyyar gina majami'a a wurin.

Ministan cikin gidan yahudawan sahyoniya Arbel ya yi gaggawar mayar da martani ga kalaman Benguir inda ya ce: Ya kamata Netanyahu ya gaggauta dakatar da Benguir dangane da masallacin Al-Aqsa. Kalaman nasa suna barazana ga salon dabarun yakinmu da Iran.

Lapid, shugaban jam'iyyun adawa a majalisar dokokin yahudawan sahyuniya, shi ma ya mayar da martani ga kalaman Benguir ya kuma ce: "Dukkan yankin ya shaida raunin Netanyahu a kan Benguir saboda ba zai iya sarrafa majalisar ministocin ba har ma matakin na Benguir ya dauka zai iya raunana tsaron cikin gida ya zamo Babu wata manufa ko dabara, babu majalisar ministoci.